Akalla ’yan bindiga 38 ne suka sheka lahira a luguden wuta da jami’an tsaro suka yi musu a Jihar Katsina, a yayin da ’yan sanda biyar suka kwanta dama.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Sanusi Buba, ya bayyana ne a lokacin da yake sanar da cewa rundunar ta cafke mutum 999 da ake zargi da aikata manyan laifuka 608 a jihar a shekarar 2021 da ke nade tabarmarta.
- Idan Buhari ya rattaba hannu a kan Kasafin Kudi na 2022…
- Najeriya A Yau: Yadda ’yan bindiga ke samun bayanan sirri
Ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, “An samu nasarar kashe ’yan bindiga 38 an kuma kashe mana ’yan sanda biyar,” a samame daban-daban da aka kai a fadin jihar a 2021.
Kwamishinan ’Yan Sandan ya kara da cewa rundunar ta kuma kama wasu mutum 874, tuni kuma aka gurfanar da su a gaban shari’a a jihar.
Rundunar ta kuma ceto akalla mutum 215 da aka yi garkuwa da su a jihar, wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su kuma suna hannun rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Sai dai ya bayyana cewa duk da matsalolin tsaron da ake fama da su a jihar, an samu raguwarsu a shekarar 2021 idan aka kwatanta da 2020.
Ya ci gaba da cewa, “Babu shakka a wannan shekarar da ta kare an fuskanci kalubale mai yawa musamman na tsaro a Jihar Katsina, amma rundunar ’yan sandan jihar ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yi da ’yan bindiga da masu satar mutane da ’yan fashi da sauran masu aika manyan laifuka.”
Sunusi Buba ya jinjina wa Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari da daukacin al’ummar jihar bisa yadda suke taimaka wa rundunar wajen yaki da masu aikata muggan laifuka a fadin jihar.
Har wa yau, ya ba su tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da kokarin da take yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.