✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe dan bindiga sun cafke wani a Katsina

Dan bindigar da aka kama ya ce ya kashe mutane kuma yana da hannu a wasu hare-hare

’Yan sanda sun kashe wani dan bindiga, sun cafke wani bayan sun dakile harin ’yan bindiga a yankin Jabiri a Karamar Hukumar Funtua ta Jihar Katsina.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce dan bindigar da aka kama ya shaida musu cewa ya kashe wasu mutum biyu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansa.

Ya bayyana cewa “Kafin asubahin ranar Alhamis zugar wasu ’yan bindiga suka kutsa unguwar Jabiri suna harbi babu kakkautawa.

“Bayan samun kiran neman dauki ne DPO da jami’ansa suka je suka yi artabu da bata-garin, suka kashe daya daga cikinsu suka cafke wani mai shekara 25 da bindigarsa kirar AK-47.

“Wanda aka kama din ya amsa laifinsa kuma ya yi ikirarin hannunsa a hare-hare da fashi da aka kai kauyukan Tatari, Abasawa, Majewa, Bageri da sauransu da ke yankin.”