Rundunar ’Yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta kama Hashiru Baku, wanda ake zargi da kisan Janar Harold Udokwere mai ritaya.
An kashe Janar ɗin ne a lokacin da ’yan fashi suka kai hari a gidansa da ke rukunin gidaje na Sunshine Estate a Abuja, a ranar 21 ga watan Yuni.
Kwamishinan ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, Benneth Igweh, ya sanar da kama wanda ake zargi.
Idan ba a manta ba a baya rundunar ta sanar da kaka kama wasu mutum huɗu kan hannu a kisan Janar ɗin; Ibrahim Rabiu, Nafiu Jamil, Aliyu Abdullahi, da Mohammed Nuhu, duk mazauna yankin Apo a Abuja.
’Yan sandan, karkashin jagorancin CSP Victor Godfrey, sun gano maɓoyar wanda ake zargin, bisa bayanan sirri da suka samu.
Wanda ake zargin ya amsa cewar sun soki Janar ɗin da wuƙa lokacin da ya ƙi yarda su yi masa fashi.
Rundunar ta bayyana cewar wanda ake zargin na daga cikin waɗanda suka tsere daga gidan yarin Kuje.
An samo wuƙar da aka yi amfani da ita da kuma wayar Janar ɗin.
CP Igweh, ya bayyana cewa har yanzu ‘yan sanda na neman sauran ‘yan fashi biyu da suka tsere da bindigar Janar ɗin.
An kama Hashiru Baku a Jihar Kano, yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga Najeriya.