An kwashi ’yan kallo a cocin St Peters Anglican da ke yankin Eziama na Karamar Hukumar Nkwere yayin da aka kama Uche Nwosu, wani surukin Sanata Rochas Okorocha.
Yanayin yadda aka yi kamen a ranar Lahadi ne ya janyo rudani yayin da aka fara rade-radin cewa sace Mista Nwosu aka yi.
- Ma’aurata sun sayar da jaririnsu kan Naira dubu 50
- An ayyana makokin kwanaki 2 bayan kashe mutum 41 a Burkina Faso
Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya hasko yadda wasu mutane dauke da makamai suka afka wa cocin inda suka tisa keyar Nwosu da karfin tuwo yayin da yake halartar wani taron addu’o’i na mahaifiyarsa da ta riga mu gidan gaskiya.
An ji yo muryoyin wasu a cikin bidiyon suna babatun cewa “an sace Nwosu”.
Hakan dai ya sanya jita-jitar an sace Mista Nwosu ta yi wa dandalan sada zumunta inda cikin kankanin lokaci labarai ke bazuwa.
Sai dai Aminiya a ranar Lahadi ta samu tabbacin cewa ’yan sanda ne suka kama Mista Nwosu.
Jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar Imo, CSP Mike Abatamma ne ya inganta rahoton yayin zantawa da wakilinmu.
CSP Abatamma y ace an kama Nwosu amma bai yi wani karin haske doriya a kan hakan ba.
Bayanai sun ce har yanzu dai tsamin dangartaka na kara tsananta tsakanin surukin Nwosu, wato Sanata Rochas Okorocha mai wakilcin shiyyar Imo ta Yamma a Majalisar Dattawa da kuma Gwamna jihar, Hope Uzodinma.
Mista Nwosu wanda ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2019, shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar a lokacin da Okorocha ke zaman gwamna a Jihar ta Imo.
Kwanaki hudu da suka gabata ne aka yi jana’izar mahaifiyar Nwosu a yankin Eziama Obaire da ke Karamar Hukumar Nkewerre a jihar Imo.