Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta kama mijin marigayiya Fatima Alhaji Bukar da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kashe ta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
A ranar Talata ce wasu da ba a kai ga gano su ba ne suka kashe Fatima a gidanta da ke Dikechiri Bayan Gidan Dambe a Maiduguri.
- Bidiyon batsa: Ministan Tsaro da Sakataren Gwamnatin Chadi sun ajiye aiki
- Majalisa ta yi watsi da kudurin bude iyakar Najeriya da Nijar
Rahotanni sun ce wadanda suka kashe matar sun daure ta da igiya, inda suka rufe bakinta don gudun kada ta yi musu ihu tare da daba mata wuka a sassa daban-daban na jikinta, wanda a karshe ya yi sanadin mutuwarta.
Wata majiya a cikin iyalan ta ce an kama mijin matar mai suna Adam Alhaji Ibrahim ne a ranar talata da daddare, bayan Gwamna Babagana Umara Zulum ya umarci hukumomi da su mayar da gawarta zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin a fadada bincike.
A baya dai kafin umarnin Gwamnan, iyalan ta sun sanya ranar Laraba da karfe 2:00 na rana domin yi mata jana’iza a gidanta da ke Maiduguri.
Gwamnan ya bayar da umarnin a bincika tare da bankado aika-aikar tare da gurfanar da su gaban kuliya.