Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta kama daliban Makarantar Kimiyya da kere-kere da ke garin Karkana a karamar Hukumar ’Yan Kwashi da ke Jihar Jigawa su 12 bisa zarginsu da kisan wani dalibi dan shekara 17 mai suna Hamisu Ado.
Kakakin Rundunar, SP Audu Jinjiri ya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yanzu sun kama daliban tare da mika su zuwa sashin bincike na rundunar ana yi musu tambayoyi.
Ya ce kamar yadda aka shaida musu, dalibin ya rasu ne sakamakon zalunci irin na ’yan makaranta.
SP Jinjiri ya ce da zarar ’yan sanda sun kammala bincike za su gurfanar da daliban da ake zargi da hannu a kisan Hamisu Ado a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
“Idan aka kammala bincike, wadanda ba su da hannu a rasuwar Hamisu Ado za a sake su. Kuma an kai gawar marigayin asibitin ’Yan Kwashi domin likitoci su gudanar da bincike kan dalilin rasuwar dalibin domin zai taimaka wa ’yan sanda kan gano sanadin rasuwar dalibin kafin a mika wa iyayen marigayin gawar dansu domin su yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Da yake karin haske kan lamarin Kakakin karamar Hukumar ’Yan Kwashi, Malam danjuma Kwarare, ya ce gaskiya ne lamarin ya faru a makarantar, amma har zuwa lokacin babu wani dalili da hukumar makarantar ta fada da za a iya yarda da shi a matsayin wata madogara da za a ce ga abin da ya yi sanadin rasuwar dalibin.