✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama bindigogi da aka boye a asibiti

Rundunar ’yan sanda mai yaki da fashi da makami (SARS) na ci gaba da binciken wasu mutum 7 da ta kama bayan gano wasu bindiga…

Rundunar ’yan sanda mai yaki da fashi da makami (SARS) na ci gaba da binciken wasu mutum 7 da ta kama bayan gano wasu bindiga da aka boye a wani asibiti mai zaman kansa da ke garin Kubwa Abuja, lamarin da ya faru a ranar Larabar makon jiya kamar yadda wata majyar ’yan sanda da ke da nasaba da lamarin ta bayyana.

Al’amarin ya biyo bayan kama wani ne a yankin birnin na tarayya a lokacin da yake kokarn yin sabbin takardu na wata mota da aka sata, sannan bayan tsananta bincike sai ya jagoranci ’yan sandan zuwa asbitin.

Wakilinmu da ya ziyarci asibitin wanda ke yankin Phase 3 a garin na Kubwa a ranar Talatar da ta gabata, ya tarar da asibitin na ci gaba da kasancewa a rufe, inda wasu mazauna unguwar suka bayayna yadda ’yan sandan suka je wajen. Wani mazaunin unguwar da bai son a ambaci sunasa ya bayyana wa Aminiya cewa jami’an tsaron wadanda suka iso wajen da misalin karfe 11 na safiyar ranar, sun shafe kamar awa guda suna gudanar da bincike a cikin asibitin, inda a karshe suka fito da bindigogi 4 da alburusai da safar fuska da kuma wasu kayayyaki na asibitin, suka sa a motocinsu biyu, sannan suka rufe asibitin.

Bayanai sun ce babban daraktan lafiya na asibitin, wanda baya wajen a yayin gudanar da aikin na ci gaba da guje wa kamun ’yan sanda. Da aka tuntube shi, babban jami’in ’yan sanda na Kubwa C.S.P Ayobami Surajudeen wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa ’yan sandan sun sanar da ofishinsa shirin aiwatar da aikin a lokacin da suka zo.