’Yan sanda sun hallaka wani shugaban kungiyar asiri da ya yi kaurin suna a Jihar Ribas, Silas Oderereke.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko ta sanar cewa ya mutu ne a wani samame da rundunar ta kai unguwar Oderereke, a yankin Ahoada ta Yamma na jihar.
- ’Yar Sheikh Dahiru Bauchi ta zama mai ba Gwamnan Gombe Shawara
- NAJERIYA A YAU: Mece Ce Makomar Jam’iyyar APC A Jihar Kano?
Ta kara da cewa “Oderereke, wanda aka fi sani da ‘Janar,’ kasurgumin dan fashi da makami ne kuma shugaban kungiyar asiri, ya kwashe shekara hudu yana wasan buya da jami’an tsaro.
“Sai dai dubunsa ta cika lokacin da ya yi arangama da jami’an tsaro, inda ya gamu da ajalinsa.
“Oderereke shi ne shugaban kungiyar asiri ta ‘Greenlanders’, wadanda suka yi kaurin suna wajen aikata laifuka,” in ji ta.
Har wa yau, ta ce ’yan kungiyar na da hannu wajen fashi da makami, kwace da kuma kashe mutanen da ke adawa da su a jihar.
Kakakin ta bayyana cewa wasu shugabannin kungiyar guda biyu, Danger Boy da 2-Man, sun tsere bayan ganin an kashe uban gidansu.
Iringe-Koko ta ce rundunar ta kwato bindiga kirar G3 da harsashi guda 19 daga maboyar ’yan kungiyar.