’Yan sanda sun dakile wasu ’yan bindiga da ke shirin kai wa jami’an Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) hari a yankin Karamar Hukumar Nnewi ta Kaudu a Jihar Anambra.
Kakakin rundunar ’yan Sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa mazauna yankin ne suka shirya kai harin.
- Ina rokon ’yan Najeriya su bari tsarin canjin kudi ya yi aiki —Emefiele
- Mai ciki ta rasu a asibiti a Kano saboda rashin sabbin kudi
Ikenga ya ce ranar Alhamis da misalin karfe biyar na yamma jami’ansu sun kubutar da wasu jami’an INEC da ke bakin aiki daga cutarwar wasu ’yan bindiga a yankin.
Jami’in ya ce sun yi nasarar dakile harin ba tare da an samu asarar rai ba.
Ya ba da tabbacin jami’ansu su za su ci gaba kokari wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu a cikin al’umma.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba.
(NAN)