✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano

Rundunar ta ƙwato kuɗin ne bayan cafke waɗanda suka yi garkuwa da mutumin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano,m, ta ƙwato kuɗi Naira 4,850,000 tare da mayar da su ga wani mutum da aka sace, bayan sun ceto shi.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutumin ne a garin Zakirai, a Ƙaramar Hukumar Gabasawa.

Masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa Naira miliyan 15 kafin daga bisani jami’an tsaro suka shiga lamarin.

“Bayan samun labarin garkuwar, jami’anmu sun ƙaddamar da bincike, inda suka kama mutum biyar da ake zargi, sannan suka ceto wanda aka sace a ranar 17 ga watan Maris,” in ji sanarwar.

An mayar da kuɗin ne ta hannun shugaban Ƙaramar Hukumar Gabasawa, Sagir Usman Abubakar, wanda ya bayyana godiyarsa a madadin wanda aka sace da mutanen yankin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai, ta hanyar kai rahoton duk wani abu da suke zargi domin daƙile ayyukan miyagu a Kano.