’Yan sanda a sun kubutar da wata karamar yarinya da aka kulle a cikin a keji tsawon wata takwas.
Yarinyar mai suna Joy Emmanuel, mai shekara 12 ta bayyana cewa an rika hana ta abinci tsawon wannan lokaci.
- Badakalar $65: ICPC na neman surikin Buhari ruwa a jallo
- JAMB: Akwai yiwuwar sauya lokacin jarabawar UTME
- Yadda aka yi Hawan Sallah a Fadar Sarkin Zazzau
- An cafke shugaban ’yan bindigar Neja
Rahotanni sun bayyana yadda gwaggon, yarinyar da mijinta da ke da zama a unguwar Sakkwato Cinema a Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa ke azabtar da yarinyar.
Bayan tonuwar asirin ma’auratan, sun shaida wa ’yan sanda cewa yarinyar na fama da tabin hankali, amma da aka gudanar da bincike aka gano cewa karya suke yi.
Kakakin ’yan sandan jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya ce an ceto yarinyar tare da tsare wanda suka rufeta a caji ofis din da ke Dadin Kowa.
“Sun tsare yarinyar cikin wani keji da ke cikin gidansu na tsawon wata takwas ba tare da isashshen abinci ba.
“Bayan jami’anmu sun balle kejin, yarinyar ta kasa tafiya saboda tsananin yunwa da ya galabaitar da ita.
“Mun same ta cikin wani mummunan yanayi, inda a ciki kejin da aka kulle ta take bayan gida da fitsari.
“Amma daga baya mun dauke ta zuwa asibitin kwararru don duba lafiyarta,” a cewar kakakin ’yan sandan.
Kazalika, ya ce za a mika yarinyar da wadanda suka daure ta ga Hukumar Hana Fataucin Mutane da Dangoginsu ta Kasa (NAPTIP), don daukar matakin da ya kamata.