Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ceto akalla mutum 97 da aka yi garkuwa da su a dajin Shinkafi zuwa Tsafe a jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ayuba El-Kana ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Gusau ranar Talata.
- Amaryar da aka sace ana tsaka da bikin daurin aurenta ta kubuta
- Da zan samu na kammala rubuta littafina da burina ya cika- Bashir Tofa, a hirarsa ta karshe
El-Kana ya ce an yi nasarar ceto mutanen ne sakamakon luguden wutar da jami’an tsaro ke yi a yankunan Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji, wadanda kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ya addaba.
A ranar 3 ga watan Janairu, 2022 ne jami’an tsaro suka samu labarin ganin wasu mutane da ake zargin sace su aka yi a cikin dajin da ke yankin Shinkafi.
A sakamakon haka, hadin gwiwar jami’an tsaro da tubabbun ’yan bindigar yankin da ’yan banga suka shiga dajin, inda suka ceto mutum 68 a dajin.
Kwamishinan ya ce mutanen sun dauki tsawon wata uku a hannun wadanda suka yi garkuwa da su — maza 33, mata 25 ciki har da masu juna biyu, sai kananan yara maza bakwai, mata uku.
Kazalika, El-Kana ya ce a ranar Litinin din ne rundunar ta musamman da aka girke a yankin Tsafe ta shiga dajin Kunchin Kalgo a Karamar Hukumar Tsafe, inda aka ceto mutum 29.
Ya ce mutanen da aka kubutar din sun shafe sama da kwana 60 a hannun ’yan bindigar da suka sace su.
Bayanai sun bayyana cewa kasurgumin dan bindigar nan Ado Aleru ne ya sace mutanen dukkansu tare da tsare su a tsawon lokacin da suka shafe a dazukan.
El-Kana ya ce wadanda aka ceto din suna asibiti inda ake ba su kulawa.
A cewarsa, za a gudanar da bincike sannan a gabatar da su ga gwamnatin jihar, kafin a mika su ga iyalansu.