’Yan sanda a Najeriya sun ceto wasu mutum takwas da aka sace a Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan.
“A kokarin da take yi na tsare rayuka da dukiyar al’umma, rundunar yan sanda a Jihar Zamfara ta tabbatar da ceto wasu mutum takwas daga hannun masu garkuwa ba tare da wani sharadi na biyan ko asi ba.
“Mutanen da rundunar ’yan sandan ta ceto an sace su ne a Kauyen Kangon Sabuwa da ke Karamar Hukumar Bungudu a ranar 25 ga watan Agusta.
“Bayan tabbatar da koshin lafiyar wadanda lamarin ya shafa an kuma mika su a hannun ’yan uwansu,” a cewar SP Shehu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito SP Shehu yana cewa, rundunar ’yan sandan za ta ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro domin kubutar da wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane.
Kakakin ’yan sandan ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bai wa ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro hadin kai a fadi-tashin da suke yi na dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar.