✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yan sanda sun cafke ’yan fashi 17 a Kano

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta cafke wasu gungun ’yan fashi wadanda suka addabi al’ummar jihar da sace-sace. Yayin da yake nuna ’yan fashin ga…

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta cafke wasu gungun ’yan fashi wadanda suka addabi al’ummar jihar da sace-sace.

Yayin da yake nuna ’yan fashin ga manema labarai, Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa rundunar ta kama ’yan fashin ne a wurare daban-daban a cikin birnin.

Gungun ’yan fashin da suka addabi al’ummar yankunan Tudun Bojuwa da Bachirawa da Kurna a cikin birnin Kano suna karkashin jagorancn Auwalu Isa, wanda aka fi sani da Lulu, mazaunin Tudun Fulani wanda kuma ya gudu daga kurkuku bayan ya shafe tsawon shekara hudu yana zaman gidan wakafi.

Sauran ’yan fashin da ak cafke sun hada da Naziru Yahaya wanda aka fi sani da John Cena mazaunin Layin ’Yan Kifi a Unguwar Kurnar-Asabe, wanda kuma bai jima da fitowa daga gidan maza ba. Haka kuma akwai Ukasha Ibrahim, wanda aka fi sani da Saleh, mazaunin Layin ’Yan Kifi da kuma Shehu Rabi’u, wanda aka fi sani da Shehi.

Majiya ya bayyana cewa an kama ’yan fashin dauke da wukake da gatari da almakashi, inda suka shiga gidan wasu sabbin ma’aurata, suka sace masu kudi da wayoyi da kayan lefen amaren da sauran kayayyaki masu daraja.

’Yan fashin sun sace wa wani mutum babur kirar Lifan. “Ba wai a nan suka tsaya ba, domin a kwanan baya sun yi kokarin kashe wani mutum mazaunin yankin mai suna Alhaji Hamza Ibrahim, inda suka yi sanadiyyar raunata shi,” inji Majiya.

Har ial yau, rundunar ta bayyana cewa ta cafke wasu ’yan fashin da suka addabi al’ummomin yankunan Sheka Barnada da Shekar Mai daki da Shekar Gidan Kaji da Bubbugaji da Chabanau da Gidan Maza da Sabuwar Gandu da Maidile duk a yankin karamar Hukumar Kumbotso, inda suke amfani da makaman da suka hada da wukake da gatari, suna tare mutane a kan hanya tare da kwace musu kudi da wayar hannu.

Majiya ya kara da cewa kasancewar dukkanin ’yan fashin sun amsa laifukansu, da zarar rundunar ta kammala bincke za a gurfanar da su gaban kuliya.