A makon nan ne aka ga hotunan Sheikh Alƙali Zariya ya halarci zauren tattaunawa na fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, wanda ake kira ‘Gabon Talkshow’, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.
Gabon Talkshow dandali ne da jaruma Hadiza ke gayyatar mashahuran jarumai da mawaƙa domin tattauna game da rayuwarsu da ayyukansu a masana’antar nishaɗi.
- Tsaro: Tinubu ya ƙaddamar da rundunar tsaron daji a faɗin Najeriya
- Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS
Bayyanar Sheikh Alƙali a wannan dandali ya jawo suka mai tarin yawa daga al’umma.
Wasu na ganin bai dace da matsayin malami irinsa ya halarci irin wannan dandali ba, domin ba wajen ilmantarwa ba ne ko karantarwa.
A cewar wasu, hakan zai iya rage darajar malamai a idon jama’a.
Sai dai kuma wasu na ganin babu laifi a yi hakan, tun da zauren tattaunawa ne da ake gayyatar mutane shahararru domin bayyana wasu ɓangarori na rayuwarsu da mutane ba su sani ba.
Wasu sun ce yin hakan na ƙara kusantar da malamai da jama’a ne.
Hakazalika, wasu sun ce ba Sheikh Alƙali ne malami na farko da ya halarci zauren Hadiza Gabon ba.
An ruwaito cewa a baya, jarumar ta taɓa gayyatar Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ma ya halarta.
Sai dai duk da haka, akwai wasu daga cikin magoya bayan Sheikh Alƙali da suka bayyana rashin jin daɗinsu kan amsar goron gayyatar Hadiza Gabon.
Sun nuna damuwa da irin suka da zagi da ya biyo bayan halartar shirin da malaminsu ya yi.
Wani daga cikin magoya bayan Sheikh Alƙali, mai suna Ibrahim G. Lamara, ya wallafa a shafinsa na Facebook yana cewa: “Mu ‘yan Izala tsagin Jos, mu da su Yaseer Haruna Muhd, lallai ba ma jin daɗin zagin da Malam Alƙali Zariya yake janyo mana. Muna fata shugabanci zai yi maganin abin a wannan karo.”
Bayyanar Sheikh Alƙali a wannan zaure ya ƙara jaddada yadda malamai da mashahuran mutane ke fuskantar ɓangarori daban-daban daga al’umma, musamman a zamanin da kafafen sada zumunta ke da tasiri wajen bayyana ra’ayoyi cikin sauƙi.