✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke matashi kan zargin kashe uwa da danta a Adamawa

Ana zargin matashin da kashe matar da danta a rafi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta cafke wani matashi mai shekara 18 da ake zargi da kashe wata mata da danta a kauyen Sabon-Layi da ke Karamar Hukumar Lamurde a Jihar.

Kakakin Rundunar a Jihar, Suleiman Nguroje, ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Yola, inda ya ce wanda ake zargin da matar duka mazauna kauyen na Sabon-Layi ne.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya farmaki matar mai suna Talatu Alhaji Usman da dan nata ne lokacin da suka je wanka a rafi.

Kakakin ya ce rundunar ta Jihar ta cafke matashin a ranar shida ga watan Yunin 2022 a garin Lamurde.

“Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa a ranar shida ga watan Yuni, 2022 ta cafke wani dan shekara 18 bisa zargin yi wa wata Talatu Alhaji Usman mai shekara 36, da danta dan shekara daya kisan-gilla a Karamar Hukumar Lamurde.

“Rahotanni sun bayyana cewar matashin ya yi yunkurin yi wa matar fyade, bayan rashin nasara sai ya tura ta cikin ruwa wanda hakan ya yi ajalinta

“Wanda ake zargin ya danna kan dan nata a cikin ruwa har sai da shi ma ya daina numfashi.

“Matashin ya shiga hannu bayan da mijin matar ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda da ke Karamar Hukumar ta Lamurde,” a cewar Kakakin.

Ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sikiru Akande, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

%d bloggers like this: