’Yan sanda sun kama wasu matasa bakwai kan laifin yin sojan gona da kuma layu 582, a garin Kaltungo a jihar Gombe
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce dubun waɗanda ake zargin ta cika ne inda aka kama su da makamai da tabar wiwi da tulin kwayoyi daban-daban.
Ya ce an kama matasan, masu shekaru 17 zuwa 21 ne a wani samame da ’yan sanda suka kai wata maboya a kasuwar garin Kalarin da Baganje a Karamar Hukumar Kaltungo, a ranar 3 ga watan Disamba 2023.
Ya ce abubuwan da aka a wajen su a matsayin kayan shaida sun hada kakin soja guda daya da hula hana-sallah, gidan harsashin bindiga kirar AK 47, da takubba da wukake da kuma gatari.
- Kano: Abba ya nada Darakta-Janar kan tallace-tallace a titi
- Harin Mauludin Kaduna ba kuskure ba ne —Sheikh Gumi
Sauran sun hada wukake da kwayar exzol, kulli 19 na tabar wiwi, kati 40 na kwayar Tramadol, layu guda 582, da kuma wata riga da aka dinka ta da layu.
Daga nan sai ya ce akwai sauran matasan da zargin, wadanda rundunar ke ci gaba da kokarin kamo su domin fuskantar shari’a.