Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aika da sakon taya murnar Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi, yana kira gare su da su rungumi darajoji na sadaukarwa, biyayya da hakuri irin wanda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna.
A wata sanarwa da Daraktan Yada labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamnan ya yi kira da a yi addu’o’in zaman lafiya da haɗin kan Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.
Ya jaddada muhimmancin nuna soyayya, tausayi da zama mai ƙyau da maƙwabta a rayuwar yau da kullum.
“Yayin da muke murnar Babbar Sallah, mu yi tunani kan abin da take nufi biyayya, sadaukarwa da ƙwarin gwiwa,” in ji Gwamna Yahaya, yana mai ƙarfafawa al’umma da su ci gaba da tallafa wa shugabanci a matakai daban-daban.
Gwamnan ya yaba wa shugabannin gargajiya da na addini bisa goyon bayansu tare da tabbatar da kudirinsa na kammala ayyukan ci gaba da aiwatar da sabbin manufofi masu alfanu.
Haka kuma, ya taya Alhazai Musulmi murnar kammala aikin Hajji, yana yi musu addu’ar dawowa lafiya da samun albarkar wannan ibada.