✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Mauludin Kaduna ba kuskure ba ne —Sheikh Gumi

Idan harin bom na farko da aka kai wa masu Mauludi kuskure ne, na biyun da aka jefa kan masu aikin cetonsu bayan minti 30…

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi zargin da gangan jirgin sojoji ya kai harin bom kan masu taron Mauludi a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.

Sheikh Ahmda Gumi idan har harin bom na farko da jirgin sojan ya aka kai wa masu Mauludin kuskure ne, to me ya sa bayan minti 30 suka jefa bom na biyun a kan masu aikin ceton wadanda aka jefa wa bom din farko?

Ya bayyana cewa “Mutanen sun ce bayan an kai wannan hari an kashe mutane, sun je suna kokarin kwashe wadanda suka rasu, sai bam na biyu ya sauka. Idan bam din farko kuskure ne, bam na biyu kuma fa?

“Muna kuma fatan wadanda suka rasu sun yi shahada, amma kada wani ya fada min cewa wai kuskure ne, a’a da gangan ne. Don haka duk wanda ya jefa wannan bom ya kamata a fito da shi.”

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana haka ne a majalisar karatunsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Malamin ya ce  ko a lokacin yaki ba daidai ba a kai wa mata ko kananan yara ko tsofaffi  hari, amma duk da haka sojoji suka kai musu hari, bisa zargin iyalan ’yan ta’adda ne.

Ya ce abin da ya faru a Tudun Biri, Allah ne Ya fallasa irin barnar da sojoji suke aikatawa a cikin dazuwa a yakin da suke yi da ’yan ta’adda.

Sheikh Gumi ya ce, “Mutane da yawa an kashe su a baya babu wanda ke magana har sai da harin ya zo kusa da gari.

“Na sha fadi cewa duk abin da ke tsakaninmu ko ’yan fashin daji ko Boko Haram akwai bukatar sulhu, amma wasu na cewa a’a a kashe su.

“A wannan kasar babu wanda zai fada min. Na yi kokarin nemo mafita amma an ki goyon bayan mu. Gwamnatin wani lokaci tana tunanin yaki, wani lokacin kuma sulhu.

“Wadannan mutane sun taru mata da yara, amma jirgin wanda ke da kemara ya je, kuma sun ga mutanen, amma suna tunanin mata da yaran wadancen mutanen ne. Kuma da a ce hakan ne da kuma shiru za ku yi.

“Amma da yake an samu kuskure an kashe wadanda ba su ake son kashewa ba. Mu a wurinmu ba mu son a kashe kowa, saboda harum ne kashe mata da yara da tsofaffi. Kuma ba mu goyon bayan irin hakan ko da kuwa ’an IPOB ne.

“Muna kuma fatan wadanda suka rasu sun yi shahada, amma kada wani ya fada min cewa wai kuskure ne, a’a da gangan ne. Dan haka duk wanda ya jefa wannan bom ya kamata a fito da shi.”