✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fastoci sun ziyarci wadanda harin bom din Mauludi ya shafa a asibiti

Fastoci sun kai ziyara domin jajanta wa wadanda iftila'in harin bam din jirgin soji ya shafa a Asibitin Barau Dikko inda suke karbar magani.

Fastoci sun kai ziyara domin jajanta wa wadanda iftila’in harin bam din jirgin soji ya shafa a Asibitin Barau Dikko inda suke karbar magani.

Jagoran masu ziyarar, Fasto Yohanna Buru, ya ce, makasudin ziyarar shi ne domin yi wa marasa lafiyar addu’ar samun sauki tare kuma da jajantawa.

Aminiya ta ruwaito cewa harin bam din a kauyan Tudun Biri a Karamar Hukumar Igabi ya tayar da hankalin mutanen kasar nan matuka.

Akalla mutum 100 ake ganin sun rasu bayan wani jirgin soja maras matuki ya sakar masu bam har sau biyu a wurin Taron Maulidi.

Fasto Buru ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu Ya kuma sa mutuwar shahada suka yi.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta yi dukkan mai yiwuwa wurin tallafa wa wadanda abin ya shafa domin rage masu radadi.

Shi ma da yake jawabi a wurin, Fasto George John cewa ya yi dalilin ziyarar shi ne domin yi wa marasa lafiyar addu’a tare da fatan samun sauki cikin hanzari.