✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke mai safarar mutane a Kaduna

Rundunar ta ce za su gurfanar da mutumin idan suka kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta cafke wani mutum da ake zargi da safarar mutane a jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai (NAN), a ranar Lahadi.

Hassan ya ce “A ranar 1 ga watan Maris, da misalin karfe 9 na safe ne Misis Jummai Danjuma da wasu mutum biyu sun shigar da kara a yankin Katari da ke Karamar Hukumar Kachia a jihar.

“A ranar 27 ga watan Fabrairu, wanda ake zargin, wanda mazaunin Ankwa ne a Karamar Hukumar Kachia, ya yi safarar matasa biyar daga Katari zuwa Eruku a Jihar Kwara don yin aikatau a wata masana’anta.

“Da isa, wanda ake zargin ya dauki matasan zuwa wata gona a Eruku, inda ya bar su a can ya koma Katari.”

Hassan ya ce daga cikin matasa biyar da aka yi safarar su zuwa Kwara guda uku sun dawo gida wajen iyayensu.

Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin gano inda sauran matasa biyun suka shiga.

Kakakin rundunar ’yan sandan, ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, bayan sun kammala bincike.