✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar NURTW ta tallafa wa mutane 360 a Kaduna

Kungiyar ma'aikatan sufuri ta NURTW ta ba wa mutane 360 tallafin kudade da turamen zani domin rage musu radadin tsadar rayuwa a Jihar Kaduna

Kungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Kasa (NURTW) ta ba wa mutane 360 a Jihar Kaduna tallafin kudade da turamen zani don rage musu radadin tsadar rayuwa a sakamakon cire tallaifin mai da gwamnati ta yi.

Shugaban NURTW Reshen Jihar Kaduna, Alhaji Tanimu Aliyu Zaria, ya ce sun dauki matakin ne domin tallafa wa mutane a daidai wannan lokaci da rayuwa ta yi tsada.

“Duk wani taimako ko tallafi da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa ba ya kawowa ga ’ya’yan kingiyarmu, saboda haka muka ga ya dace mu ma kanmu ’yan kungiya mu ririta abin da muke samu taro da sisi domin tallafa wa matan da suka rasa mazajensu da masu karamin karfi da kuma maza,” inji shi.

Daga cikin matan da suka amfana akwai wadanda suka sami N10,000 da turmin zani kowaccensu, sai masu N10,000 kawai, sai kuma maza 323 da suka amfana da wadannan kudade.

Shugaban kungiyar ya bukaci gudunmawa daga gwamnatin jihar Kaduna da kuma tarayya saboda irin ayyukan da suke gudanarwa.

Sannan ya yi kira ga mambobin kungiyar da a kodayaushe suka rika ba shugabannin goyon baya domin samun cigaba.

A nasa jawabin, daya daga cikin shugabanin kungiyar a Kaduna, Alhaji Lawal Abubakar, ya ce aikin tallafin yanzu suka fara, saura rukuni na biyu da na uku da ke tafe a wannan lokacin da masu karamin karfi suke bukatar taimako.

A cewarsa, wannan kadanne daga cikin Ayyukan kungiyar ta NURTW a Kaduna, saboda ta dade tana tallafa wa mabukata.

Wadanda suka amfana dai sun bayyana godiyarsu da jin dadi ga kungiyar NURTW da shugabanninta na jihar, bisa yadda suka dube su a wannan lokaci na tsadar rayuwa da talakan Najeriya ke fama da yadda zai samun abin da zai ci.