Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya kaddamar da rabon kayan abinci a karo na 17 ga marasa galihu da nakasassu kimani dubu ɗari biyu da sha hudu da dari biyar.
Za a yi rabon kayan abincin ne a rumfunar zabe guda dubu 2,218 da ke mazaɓu 114 a fadin jihar.
Gwamnan ya ce, ya fara ba da irin wannan tallafin ne tun a zangonsa na farko, inda ya raba sau 15.
Ya ce a yanzu bayan dawowarsa wannan shi ne karo na biyu kuma jimilla na 17 idan an hada da wanda ya yi a baya.
Gwamnan ya kira al’ummar jihar Gombe da su ci gaba da taimaka wa juna da dan abin da suke samu.
- ‘Za mu soma Itikafi tunda bizar Umrah ta gagara samu’
- Za a saki mutum 200 da aka wanke daga zargin alaƙa da Boko Haram a Borno
Ya kuma roki da su ci gaba da yi wa Jihar Gombe da Najeriya addu’ar dorewar zaman lafiya.
A jawabinsa, shugaban kwamitin rabon kayan abincin wanda shi ne Mataimakin Gwamnan jihar, Dokta Manassah Daniel Jatau da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Abubakar Inuwa Kari ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar tana sane da irin matsalolin tattalin arziƙin da al’ummar jihar ke fuskanta musamman na ƙarancin abinci.
Ya ce, abin ya sa aka kafa ƙananan kwamitocin masu ruwa da tsaki a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi shi ne don tabbatar da rabon kayan abincin cikin tsanaki.
Ya yaba wa al’ummar jihar bisa natsuwa da bin doka da oda da suka nuna, duk da ƙalubalen da ake fuskanta na matsin tattalin arziƙi.
A jawabinsa na godiya a madadin waɗanda suka rabauta da tallafin, Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar na III, ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa taimakon marasa galihu musamman a wannan lokaci na taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
Ya kuma yi ƙira ga sauran ‘yan siyasa da masu riƙe da muƙamai su yi koyi da wannan karamci na gwamna Inuwa.
Tallafin abincin na wannan karo ya ƙunshi taliya, shinkafa da kuma masara.