✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za mu soma Itikafi tunda bizar Umrah ta gagara samu’

Daruruwan musulmi za su yi ibadar Itikafi a masallacin na unguwar sabuwar Madina a bana.

Shugaban kwamitin masallacin Juma’a na Sabuwar Madina da ke yankin Juwape a Maraban Gurku ta Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, ya bayyana cewa za su fara gudanar da ibadar Itikafi a masallacinsu bana. 

Malam Muhammad ya bayyana hakan ne ga jama’ar yankin a wani yunƙuri na share hawayen daruruwan mutanen da suka so tafiya Umarah amma lamarin ya gagara.

A bana dai ana fama da wahalar samun bizar Umrah, wanda hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce ba zai rasa nasaba da yadda wadansu suka karbi biza da wuri amma suka ki tafiyar ba.

Daruruwan musulmi ne dai ake sa ran za su yi ibadar Itikafi a masallacin na unguwar sabuwar Madina a bana.

Shugaban kwamitin gudanarwa na masallacin ya ce sun shirya tsaf domin karbar baki daga ciki da wajen anguwar tasu domin wannan ibada.

A cewarsa, “mun tsara takardar neman izinin shiga Itikafi ga duk mai buƙata, kuma za mu rufe karbar takardar ne a daren juma’a, 19 ga Ramadan 1445, domin tabbatar da an samar da kayan bukatar maniyyata itikafin yaddda ya kamata.”

Wani wanda ke da niyyar shiga Itikafi a anguwar ya bayyana wa wakilinmu jin daɗinsa da wannan dama a daidai wannan lokaci da tafiya kasa mai tsarki ta gagari mai ƙaramin ƙarfi.

Babban ladanin masallacin wanda mamba ne a kwamitin Itikafin, Malam Yakubu ya bayyana cewa sun samar da bandakin wanka da na zagayawa daidai da buƙatar masu Itikafi.

Ya ce za su taimaka wa masu ibadar da abin da Allah Ya hore musu, saboda “babban abin da ya ɗaukaka Makka da Madina shi ne karbar baki.

“Don haka za mu yi iya ƙoƙarinmu wurin kyautatawa bakin namu idan Allah Ya kawo su.”