Majalisar Dokoki ta Tarayya a ranar Alhamis ta amince a kashe Naira biliyan 70 a matsayin kudaden maraba ga sababbin ’yan majalisar tarayya.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kwarya-kwaryar kasafin 2022 na Naira biliyan 819.5, kuma ya samu amincewar zaurukan Majalisar Dattawa da ta Wakilai.
- Majalisa ta sahale wa Tinubu ya kashe N500bn don rage radadin cire tallafin mai
- ’Yan majalisa sun bukaci karin albashi bayan cire tallafin mai
Shugaban Kasa Bola Tinubu ne dai ya aike wa majalisun da bukatar.
Baya ga wannan kudurin ya kuma amince da kashe Naira biliyan 500 domin samar da tallafin rage radadi ga ’yan Najeriya biyo bayan cire tallafin man fetur.
Kazalika, daga cikin kudin an ware wa Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje Naira biliyan 185 domin gyara barnar da ambaliyar ruwa ta yi wa hanyoyi a shiyoyin siyasa shida da ke kasar nan a shekara ta 2022.
An kuma ware wa Ma’aikatar Noma Naira biliyan 19.2 domin ita ma ta magance matsalar ambaliyar ruwa ta bara da ta shafi gonaki.
Sauran bangarorin da aka ware wa kudi a kasafin sun hada da Hukumar Shari’a ta Kasa wacce aka ware wa Naira biliyan 35, sai Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja wacce aka ware wa Naira biliyan 10, yayin da ita kuma Majalisar Dokoki za ta kashe biliyan 70 ga sabbin mambobinta.