Rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta hana Gwamna Similanayi Fubara shiga cikinta a safiyar wannan Larabar.
Bayanai sun ce gwamnan ya ziyarci majalisar da ke yankin Aba na birnin Fatakwal ne domin gabatar mata da Kasafin Kuɗin jihar na 2025.
- Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha
- Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi
Sai dai bayan isowar gwamnan tare da tawagarsa, ya tarar da ƙofar shiga majalisar a garƙame da kwaɗo kuma an ƙi buɗewa da ke tabbatar da alamar ba a maraba da shi.
Babu wani ƙwaƙwaran dalili da aka bayar, sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an rufe wa gwamnan ƙofa ne saboda bai sanar da majalisar a hukumance cewa zai zo gabatar da Kasafin Kuɗin jihar ba.