✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago

Dakatar da zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar da rashin biyan albashin ma’aikatan keta haƙƙin bil’adama.

Ƙungiyoyin ƙwadago reshen Jihar Ribas sun yi barazanar ɗaukar mataki muddin gwamnatin Nijeriya ba ta janye dokar-ta-ɓacin da ta ayyana a jihar ba.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar gamayya da ƙungiyoyin ƙwadagon na NLC, TUC da JNC suka fitar a ranar 24 ga watan Maris.

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na jihar sun nuna damuwa kan tasirin dokar-ta-ɓacin a kan tattalin arzikin jihar da kuma nuna rashin dacewar ta a hukumance.

A cewarsu, wannan matakin ya sanya an kasa biyan albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar.

’Yan ƙwadagon sun bayyana cewa dakatar da zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar da rashin biyan albashin ma’aikatan keta haƙƙin bil’adama ne da ka iya ta’azzara matsalar tsaro da na tattalin arziki a jihar.

Sanarwar da ƙungiyoyin suka sanya wa hannun ta yi kira ga Tinubu da majalisar dokoki da kuma ɓangaren shari’a da su ɗauki matakan janye dokar nan take tare da mayar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa da kuma ’yan majalisar jihar.

A cewar ’yan kwadagon, muddin ba a yi hakan ba nan da wani lokaci, za su ɗauki matakan da ka iya shafar tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan sanarwa na ƙunshe da sa hannun shugaban NLC na Ribas, Alex Agwanwor da takwaransa na TUC, Ikechukwu Onyefuru da kuma shugaban JNC, Chuku Emecheta.