✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati

Ibas ya amince da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke.

Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas.

Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban.

Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne a daidai lokacin da Ibas ya amince da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke, yana mai gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacinsa.

Ibas ya ce naɗin Farfesa Worika ya yi daidai da manufofin sa na amfani da ƙwararru daga jihar Ribas domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A halin yanzu, an naɗa Iyingi Brown, Babbar Sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin mai riƙon muƙamin har zuwa lokacin da za a naɗa sabon shugaba.