Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa bana za a gudanar da itikafi a Masallatan Harami lokacin azumin watan Ramadan.
Shafin Haramain Sharifain ya rawaito cewa nan gaba kadan ne za a fitar da tsarin gudanar da itikafi a shafin intanet na hukumar da ke kula da masallatan biyu.
Wannan ne karon farko da za a gudanar da itikafi cikin shekaru biyu tun bayan bullar annobar Coronavirus.
A Litinin din ta gabata ce kuma mahukuntan kasar Saudiyya suka soke duk wasu matakan dakile yaduwar cutar Coronavirus, suna mai cewa duk wani maniyyaci zai iya yin aikin Hajji ko Umara ba tare da ya nuna shaidar yin allurar rigakafin cutar ko gwajin cutar ba.
Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta ce maniyyata da masu ziyara da ba su yi allurar rigakafin cutar ba za a basu damar shiga kasar muddin sun mallaki biza.
Shafin Haramain ya ruwaito cewa a Litinin din ce Ma’aikatar lafiya ta Saudiya ta sanar da cewa ta kai matakin yin allurar rigakafin Coronavirus da kashi 99 cikin 100, inda yanayin kamuwa da cutar ya ragu zuwa kashi 5 cikin 100.