✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a Saudiyya

Maniyyatan da suka kamu da cutar suna samun kulawa a asibitoci a biranen Makka da Madina

Mutum daya ya rasu bayan da maniyyata 99 daga kasar Indonesiya suka kamu da cutar lamoniya a yayin da suka tafi aikin Hajji a Saudiyya. 

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Indonesiya ta bayyana damuwa game da yawaitar kamu da cutar ta lamoniya a tsakanin maniyyatan nata.

Sanarwar da ta fitar ta bayyana cewa maniyyatan suna samun kulawa a asibitoci a biranen Makka da Madina tana mai kira da ga maniyyatan da su “kiyaye sosai, saboda lamarin na iya kara munana idan ba a yi maganinsa da wuri yadda ya kamata ba.

Shugabar Sashen Kiwon Lafiya na na Tawagar Aikin Hajjin Kasar, Liliek Marhaendro Susilo, ta danganta bullar cutar da tsananin zafi da gajiya da kuma cunkoson jama’a sai kuma matsalolin lafiya da jama’a ke fama da su.

Don haka ta bukaci maniyyata da su dauki matakan sanya takunkumin rufe fuska da wanke hannuwansu da shan ruwa sosai da kuma shan magunansu yadda ya kamata. Sauran su hada da nisantar shan sigari da kuma saurin kai rahoton duk wata matsalar lafiya da suka samu domin a dauki mataki.

A nata bangaren, Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya ta sanar cewa maniyyatanta 25,075 sun tafi Makkah daga Madina sanye da katinsu na Nusuk, wanda hukumomin Saudiyya suka wajabta wa maniyyata sanyawa a matsayin katin shaidarsu. (Xinhua/NAN)