✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke mai jinyar ’yan bindiga a Sakkwato 

An kama ma'aikacin kiwon lafiyar da AK-47 guda uku.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, ta cafke wani ma’aikacin kiwon lafiya mai shekara 35, a unguwar Badon Hanya bisa zargin sa da jinyar ’yan bindiga a jihar.

An kama ma’aikacin ne tare da wasu mutum 12 a hanyarsu ta zuwa Tambuwal domin gudanar da wani aiki.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a ranar Alhamis, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Kaigama, ya ce ma’aikacin kiwon lafiya ne, ke kula da ’yan bindigar da suka samu raunin harbin bindiga.

Kaigama, ya kara da cewa an kwato bindiga kirar AK-47 guda uku tare da harsashi guda 116 daga hannunsu.

Wanda ake zargin ya amsa cewa yana kula da ’yan bindiga a duk lokacin da suka samu rauni.

Ya bayyana cewar suna biyan sa Naira 100,000 idan ya kula da duk wani majiyanci da ya samu raunin harbin bindiga.

Kwamishinan ya ce rundunar tana ci gaba da bincike domin zakulo wasu da ke taimaka masa wajen aikata laifin.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su mika shi kotu domin girbar abin da ya shuka.