Rundunar ‘Yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, ta bukaci a kwantar da hankali yayin da ta ke gudanar da bincike kan wani rahoton hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wani rukunin gidaje da ke Kubwa.
Wata sanarwa da kakakin rundunar a Abuja, DSP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Laraba, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da maharan suka mamaye yankin, inda suka bude wuta kan mazauna yankin, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da yin garkuwa da wasu hudu.
- Qatar 2022: Yadda kasar Maroko ta daga darajar Afirka
- EFCC ta damke matashi kan damfarar baturiya N242m
A cewar kakakin, Kwamishinan ‘Yan Sandan babban birnin, Babaji Sunday, ya ce sun dauki matakin gaggawa inda suka kai wani samame na farautar wadanda suka kai harin, kuma nan take suka yi nasarar ceto mutum uku tare da kwato bindigogi da alburusai ciki har da AK-47 guda daya da harsashi 25.
Ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa masu laifin sun harbe mutum biyu, Oshodi da wani Abdulwahab.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wadanda ake zargin yayin da suke kai harin, sun yi awon gaba da mutum hudu.
“Nan da nan aka garzaya da mutanen biyun da suka harba zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu, amma abin takaici, daya daga cikinsu mai suna Oshodi, likita ya tabbatar da rasuwarsa, yayin da Abdulwahab ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.
“A halin da ake ciki kuma, Kwamishinan ya yi kira da a kwantar da hankali, sannan rundunar ta tura bayanan sirri da sauran abokan aiki don karfafa tsaro a daukacin yankin Kubwa da kewaye.
“Rundunar ta bukaci jama’a da su kasance cikin shiri da kai rahoton bayanan sirri ta lambobi kamar haka: 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883,” injin sanarwar.