Rundunar ‘yan sandan a jihar Kano na neman Salihu Sagir Takai dan takarar mukamin gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP da ya kai kansa ofishinsu yau Litinin 15 ga watan Oktoba domin kare kansa daga zargin kisan wani dattijo mai shekara 70.
Sanarwar da kakakin rundunar, Sufritenda Magaji Musa Majiya ya sanyawa hannu a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Rabi’u Yusuf na cewa ya kai kansa ofishin kwamshinan.
A ranar Asabar 13 ga watan Oktoba dan takarar gwamnan ya fito daga filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano akan hanyarsa ta zuwa gidansa tare da wasu magoya bayansa, Magoya bayan da ke cikin tawagarsa suka sari wani dattijo mai shekara 70 da haihuwa a ka a daidai shataletalen Ahmadu Bello Way, lamarin da yayi sanadin mutuwarsa.