✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda na bincike kan mafaraucin da zakuna suka cinya a Afirka ta Kudu

’Yan sanda a Afirka ta Kudu sun ce wasu zakuna sun cinye wani mafaruci tas, sai kansa kawai suka bari. An gano kan mutumin ne…

’Yan sanda a Afirka ta Kudu sun ce wasu zakuna sun cinye wani mafaruci tas, sai kansa kawai suka bari.

An gano kan mutumin ne da sauran burbushin jikinsa a yashe kusa da wata bindiga irin ta mafarauta, a wani gandun daji da ke kusa da Kruger da ke yankin Limpopo kamar yadda BBC ya ruwaito.

Jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta ce, mazauna yankin ne suka fara ankara cewa wani abu yana faruwa saboda ihun da suka jiyo da kuma karar harbin bindiga.

Amma lokaci ya riga ya kure ta yadda ba za su iya kai masa agaji ba.

Mai magana da yawun ’yan sandan Limpopo, Moatshe Ngoepe, ya ce: “Mutumin dai kamar farauta yake yi a gandun dajin yayin da zakunan suka kai masa hari.  Sun cinye mutumin, ba abin da suka rage a jikinsa sai kansa da burbushin sassan jiki.”

A yanzu dai ’yan sanda suna kokarin gano ko wane ne mutumin.

Sai dai babu tabbas kan ko wacce irin dabba yake farauta a lokacin da abin ya faru – amma ana tunanin ba mamaki ma farautar zakunan yake yi.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, wata 12 da suka gabata an samu gawarwakin wasu zakuna da aka ba su guba aka kuma yanke kawunansu.

Wadansu mutanen sun yi amanna cewa ana amfani da wasu bangarorin jikin zaki wajen hada maganin gargajiya.