✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda a Ogun sun hallaka masu garkuwa da mutane

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta yi nasarar hallaka wadansu  masu garkuwa da mutane da suka daɗe suna cin karensu babu babbaka a kan babbar…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta yi nasarar hallaka wadansu  masu garkuwa da mutane da suka daɗe suna cin karensu babu babbaka a kan babbar hanyar nan ta Legas zuwa Ibadan.

Masu garkuwa da mutanen su shida, sun gamu da ajalinsu ne a yayin wata musayar wuta a tsakaninsu da ’yan sanda masu yaƙi da aikata manyan laifuffuka (FSARS).

Da yake yi wa Aminiya ƙarin haske lokacin da ya jagoranci ’yan jarida zuwa ruƙuƙin dajin da aka hallaka masu garkuwa da mutanen, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya  ce rundunar ta samu nasarar hallaka su ne bayan da suka shafe kusan awa guda suna musayar wuta da su. Ya ce an raunata jami’ansu biyu, waɗanda a yanzu suke murmurewa kuma ake kula da lafiyarsu.

 “Kun ga dai yadda muka hallaka waɗannan ɓatagari da ke addabar jama’a, ga su nan dukansu a ƙasa kuna kallon su. Wannan shi ne ƙarshen duk wani ɗan ta’adda da ke neman tayar da hankalin jama’a. Mun daɗe muna fakon su. Ko a kwanaki sai da suka yi garkuwa da wadansu likitoci 2 da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar  Ibadan, koda yake mun yi nasarar kuɓutar da likitocin mun kuma sha alwashin ganin ƙarshen ɓatagarin, waɗanda a yanzu kuke ganin gawarwarkinsu guda shida a nan,” inji shi.

Ya ƙara da cewa suna yin ɗanyen aikinsu ne a kan babbar hanyar ta Legas zuwa Ibadan. Ya ce wannan hanya ce kuma mahaɗar jihohin Arewa da Kudancin ƙasar nan, inda suke shiga garuruwan Ibadan na Jihar Oyo da Ore a Jihar Ondo da kuma shiyyar Ogere a Jihar Ogun; inda suke shiga da mutanen da suke garkuwa da su cikin ruƙuƙi su ɓoye su, su kuma nemi kuɗin fansa daga danginsu, idan an hana su su hallaka su. Ya ce ƙwaƙawaran bincike da rundunar ta yi ne ya ba su nasarar gano su, inda bayan hallaka su kuma aka kwato tarin makamai da kayayyakin tsubbace-tsubbace da suke tare da su.