Wasu ’yan Sa-Kai sun kashe wasu mutum 11 da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne yayin wani harin da suka kai wasu kauyuka da ke Karamar Hukumar Koton-Karfe ta Jihar Kogi.
Kazalika, ’yan sa-kan sun kuma sami nasarar cafke wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC wanda aka bayyana sunanshi da Abdullahi Sa’idu tare da wani abokinsa.
A ranar Juma’a ne dai ’yan bindigar suka kai hari yankin da nufin satar mutane amma ’yan sa-kan suka yi musu kwanton bauna.
Kazalika, a sakamakon haka, sun sami nasarar kubutar da wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su.
Aminiya ta gano cewa ana zargin jami’in na NSCDC da abokin nasa da samarwa da ’yan bindigar makaman da suke amfani da su wajen aikata ta’asar.
Mohammed Onogwu, kakakin Gwamnan Kogi, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Legas ranar Lahadi, ya kuma ce yanzu haka akwai ’yan bindiga biyar da jami’in na NSCDC a hannun hukumar tsaro ta DSS.
Ya bayyana nasarar a matsayin wata babbar ’yar manuniya kan yadda gwamnatin Jihar ta jajirce wajen magance matsalar tsaro a Jihar.
Onogwu ya kuma ce yanzu haka jami’an tsaro a Jihar na can na bin sahun wadanda suka yi garkuwa da mutane a garin Kabba na Jihar a cikin makon nan, don ganin an kubutar da su an kuma kama masu garkuwar.