Ministan Noma da Raya Karkara, Mohammed Mahmud Abubakar ya ce babu wata barazanar yunwa a Najeriya saboda mutane na da isasshen abinci a rumbunansu.
Ya ba da tabbacin ne a Abuja ranar Litinin, yayin jawabi kan nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karo na biyar.
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani
- Miyetti Allah za ta iya kawo karshen hare-haren ’yan bindiga – Sarkin Musulmi
Da yake amsa tambaya a kan hauhawar farashin kayayyaki, Ministan ya ce, “Hakika muna da wadataccen abinci a kasar nan. Babu barazanar yunwa. Na yarda farashinsu ya tashi, amma gwara tashin farashi da a ce babu ne gaba daya.
“Muna noma isasshiyar shinkafa, mu ne ma na daya a nahiyar Afirka wajen nomanta, haka ma abin yake a fannin rogo da doya.
“A bangaren noman dawa kuwa, mu ne na biyu a duniya bayan Amurka, kuma na uku a noman gero a duniya. Muna da isasshen abinci, kuma ba za mu fuskanci karancinsa ba.”
Sai dai Ministan ya alakanta tsadar takin zamanin da ake fama da ita a bana kan annobar COVID-19 da sauyin yanayi da kuma rikicin Rasha da Ukraine.
Mohammed ya kuma ce a ranar 12 ga watan Disamba mai zuwa Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da wani taron shiyya-shiyya kan rikicin manoma da makiyaya.
Ya kuma ce Gwamnatin za ta ci gaba da aikin gina rugage da burtalolin kiwo na zamani ga makiyaya.
A cewarsa, tuni aka riga aka ware wurare 16 a jihohi takwas a matsayin cibiyoyin kiwon dabbobi na kasa, kamar yadda yake kunshe a Daftarin Kiwon Dabbobi na Kasar (NLTP).