✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya da suka maƙale a Isra’ila na neman ɗauki

’Yan Najeriya mazauna ƙasar Isra’ila sun maƙale bayan ɓarkewar yaƙin Iran da Isra'ila.

’Yan Najeriya mazauna ƙasar Isra’ila sun maƙale bayan ɓarkewar yaƙin Iran da Isra’ila. Sun nemi agajin Gwamnatin Tarayya game da kan halin ƙuncin da suka faɗa tun bayan ɓarkewar yaƙi.

Cikin wani rahoto da Jaridar Punch ta wallafa, ’yan Najeriyar sun zargi gwamnati da rashin kai masu ɗauki yadda da ya kamata, inda suka ce tuni sauran ƙasashe suka fara kwashe ’yan ƙasarsu.

Rahoton ya bayyana cewa ’yan Najeriyar sun fi yawa a birnin Ƙudus da Tel Aviv, inda Iran ta tsananta kai hare-hare.

A halin yanzu, mazauna Isra’ilar sun bayyana cewa suna ɓoye ne a wurare da babu tabbas kuma rayuwarsu na cikin haɗari, a koyaushe komai na iya faruwa da su.