✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Majalisar Tarayya Sun Yanke Rabin Albashinsu

Majalisar ta amince da kudurin kuma ta aike da shi ga kwamitocin da suka dace domin zartarwa

Mambobin Majalisar Wakilai sun amince a zaftare rabin albashinsu na tsawon watanni shida saboda yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeria.

’Yan Majalisar sun yi ittifakin yanke rabin albashin nasu ne bayan  bukatar hakan da Mayaimakin Shugaban Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya bagatar.

Benjamin Okezie ya nemi kowane dan majalisar ya hakura da rabin tsurar albashinsa na N600,000 a kowane wata domin tallafa wa ’yan Nijeriya da ke cikin halin matsin rayuwar a halin yanzu.

Mataimakin shugaban majalisar ya ce za a yi amfani da albasin nasu da aka yanke ne wajen taimaka wa gwamnati don magance tsadar kayan amsaraufi domin kawo saukin lamurra ga al’ummar kasar.

Kalu ya gabatar da wannan bukata ne a kan rokon da Honorabul Isiaka Ayokunle ya yi ga masu shirin gudanar da zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa, cewa su janye su hau teburin tattaunawa da gwamnati.

Da wannan yanke rabin albashi da ’yan majalisar su 360 suka yi, a duk wata za su hakura da jimillar kudi Naira miliyan  108.

A tsawon watanni shida kuma, jimillar abin da za a yanke musu shi ne Naira miliyan 648.

Majalisar ta amince da kudurin kuma ta aike da shi ga kwamitin kasafi kudade da ayyukan jin kai domin aiwatar da yanke albashin mambobin.