Ministan Shari’a na Kasa kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami ya ce yunkurin da ’Yan Malalisar Wakilai ke yi na gayyatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ya kan doron doka kuma ba su da hurumin yin haka.
A cewarsa, kundin dokokin Najeriya ya ba ofishin shugaban cikakkiyar dama ta adana bayanan tsaro na sirri ba tare da bayyana su ga kowa ba.
- Matsalar Tsaro: Buhari ya gana da Gwamnoni 36 na Najeriya
- Rashin tsaro: Buhari zai bayyana a gaban Majalisa ranar Alhamis
Martanin Ministan na zuwa ne bayan wani yunkuri da Majalisar take yi a kwanan nan na gayyatar Buharin zuwa gabanta domin yin bayanin a kan irin kalubalen tabarbarewar harkokin tsaro a kasa.
A baya dai Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila ya ce shugaban ya amince ya bayyana gabansu domin yi musu bayani.
Amma Malami ya ce, “Damar Shugaban Kasa ko amincewa ya bayyana a gaban Majalisa abu ne da ya rataya a wuyansa shi kadai ba wai na majalisar ba.
“Gudanarwa da kuma kula da harkokin tsaron kasa aikin Shugaban Kasa ne shi kadai, kamar yadda sashe na 218 (1) na Kundin Tsarin Mulki ya yi tanadi a matsayin sa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya.
“Duk wani yunkuri na gayyata domin yayata wadannan bayanai ko kuma kwarmata su ta hanyar yi masa titsiye wani yunkuri ne na wuce gona da iri a bangaren Majalisar.
“A matsayin sa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Shugaban Kasa ne kadai ke da damar sanin sirrin tsaron kasa.
“Saboda haka, ta hanyar gayyatar shugaban domin tattauna batutuwan tsaro, Majalisar na kokarin wuce hurumin ta ne,” inji Minista Malami.