Wani kusa a hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) daga Jihar Yobe Alhaji Muhammad Sani Fema ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne samun nasarar da kungiyar kwallon kafa na ‘yan kasa da shekaru 17 suka yi na kare kambun su na sake dauko kofin gasar kwallon kafa na duniya da aka yi a kasar Chile.
Alhaji Muhammad Sani ya bayyana haka ne ga Aminiya a garin Damaturu dangane da hazakar da matasan suka nuna na sake kare kambunsu da suka yi a gasar duniya da aka gudanar a kasar Chile a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ci gaba da cewa, kamar yadda aka sani tun farkon fara gasar matasan suka nuna wa duniya cewa ba sun je Chile don yawon bude ido ba ne, sun je ne don kokarin sake dawo da kofin kasar su Najeriya a matsayin su na wadanda suka kware kuma masu kishin kasa.
Jami’in na hukumar kwallon kafar ya kara da cewa, wannan rawar gani da wadannan matasa suka yi ya yi matukar faranta zuciyar dukannin al’ummar kasar nan da kuma Nahiyar Afirka da duniyar bakar fata baki daya.
Da Aminiya ta tambaye shi ko akwai wani shirin karfafa gwiwa da gwamnatin kasar nan ta yi ga matasan? sai ya ya ce, lallai akwai alamar hakan domin mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari kwana daya kafin su buga wasan karshe ya kira su daya bayan daya ta na’urar zamani suka gaisa tare da yaba musu kuma ya yi hakan ne don karfafa musu gwiwa. Wannan ya nuna shugaban yana sane da su, kuma zai saka musu da alheri.
’Yan kwallon Eaglets sun yi rawar gani – Sani Fema
Wani kusa a hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) daga Jihar Yobe Alhaji Muhammad Sani Fema ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne samun…