✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Afirka 10 Da Suka Yi Bajinta a 2023

Aminiya ta yi duba kan 'yan wasa 10 da suka nuna bajinta a 2023.

A shekarar nan ta 2023 da ke bankwana, ’yan kwallon kafar Afirka, babu shakka sun baje kolin hazakarsu a matakai daban-daban, inda suka nuna gogewa a fadi duniya.

A ’yan shekarun baya a iya cewa ’yan kwallon da Afirka ke kyankyashewa sun zama abun alfahari, kuma suna fidda ba wa marada kunya.

Wannan ta sa Aminiya ta zakulo wasu ’yan wasa da suka taka rawar gani a 2023, inda suka ba wa kungiyoyin da suke murza leda da kuma kasashensu gudunmawa wajen kafa tarihi, lashe kofuna ko kyautuka a 2023.

Wadannan ’yan wasa su ne kamar haka:

1. Victor Osimhen

A 2023 dan wasan gaban Super Eagles na Najeriya da kuma kungiyar Napoli da ke kasar Italiya, ya taimaki Napoli wajen lashe gasar Serie A a karon farko cikin shekaru 30.

Sannan shi ne ya lashe Gwarzon Dan Kwallon Kafar Afirka na 2023, inda ya doke dan wasan gaban Masar, Mohamed Salah da dan wasan bayan Maroko, Ashraf Hakimi.

Har wa yau, a 2023 Osimhen ya jefa wa Napoli kwallo 41 a wasanni 45 da ya buga mata.

A gida Najeriya kuwa, Osimhen ya zura wa Super Eagles kwallo 20, wanda da haka ya zamo na biyu wajen jeri jefa wa Super Eagles kwallo, bayan tsohon Rashidi Yakini wanda ke da kwallaye 37.

Sunan tauraron Osimhen ya haska a idon manyan kungiyoyin turai, Chelsea, Manchester United, Real Madrid, PSG, da Juventus ke rububin daukar a kakar wasanni mai zuwa.

2. Asisat Oshoala

Asisat Oshoala ’yar kwallon Najeriya ce da kuma kungiyar mata ta Barcelona da ke kasar Spain, ta yi zarra a fagen kwallon kafar mata a Afrika har da nahiyar turai.

Oshoala dai ita ce gwarzuwar ‘yar kwallon kafar Afrika ta mata, inda ta doke ’yan wasa irin su Thembi Kgatlana ta kungiyar Racing Louisville da Barbra Banda ta kungiyar Shanghai Shengli.

Wannan shi ne karo ma shida da Oshoala ke lashe kambun gwarzuwar ‘yar kwallon Afrika ta mata.

A 2023, Oshoala ta lashe gasar zakarun Turai ta mata da kofin Super Cup na mata, sannam ta zura kwallo 26 sannan ta taimaka a ci kwallo shida a raga.

Har wa yau, ’yar wasan ta kare a mataki na 20 a jerin ’yan wasan da aka ware domin fafatawa wajen lashe kyautar Ballon d’Or ta 2023.

Oshoala ta kasance jagora a cikin ’yan wasan kwallon kafar mata ta Najeriya suka nuna bajinta a gasar kofin duniya ta mata da aka yi a kasar Austria da New Zealand.

Fitacciyar ’yar wasan duk da fama da rauni da ta yi, amma ta taimaka wa kungiyar ta Barcelona da kuma tawagar ‘yan wasan kwallon kafar mata ta Najeriya.

3. Mohamed Salah

Salah, dan wasan gaban Masar ne da kuma Liverpool da ke Ingila ya zamo wa kasarsa da kungiyarsa gwarzo, musamman a kakanin wasanni biyu a jere , inda yake ci gaba da jan zarensa babu kakkautawa.

A watan Satumba Salah ya kafa tarihin zama dan Afirka da ya fi taimakawa a zura kwallo a gasar Firimiyar Ingila.

A kakar wasanni da suka wuce a jere, kowannensu dan wasan ya jefa kwallo sama da 30 a raga, da hakan ya sa ya zura wa Liverpool kwallo sama da 100.

Salah ya ci gaba da zama jigo ga kasarsa ta Masar a duk lokacin da za ta kara wasa.

Yanzu haka dan wasan ya ci wa Liverpool kwallo 23, sannan ya taimaka an zura 17 a shekara 2023 da ke bankwana.

4. Ashraf Hakimi

Ashraf Hakimi, dan asalin Moroko mai shekara 24 da ke taka leda a Kungiyar PSG da ke Faransa, ya shiga jerin ’yan wasa uku da aka ware domin lashe kambun gwarzon dan wasan Afrika na 2023, amma Victor Osimhen na Najeriya ya masa fintinkau.

Hakimi dan wasa ne na zamani, wanda a wasu lokuta yake iya buga wurare daban-daban a cikin filin wasa.

Hakimi ya kan iya buga baya, tsakiya ko kuma gaba a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Salon wasansa a wannan zamani ya sa dan wasan zai iya buga kowane irin salon kwallo da masu horarwa suke bullowa da su.

’Yan wasan gaba irin su Mbappe da suke murza leda a PSG da Ziyech da suke wasa a Maroko sun san irin hidimar da dan wasan yake musu wajen zura kwallo da suke yi a raga.

5. Mohammed Kudus

Mohammed Kudus dan wasan tsakiyar kasar Ghana ne da kuma kungiyar kwallon kafa ta West Ham da ke Ingila.

Amma a lokuta da dama yakan gigita abokan hamayya su rude su kasa gane shi dan wasan tsakiya ne ko dan wasan gaba saboda yadda ya lakanci murza kwallo da kuma jefa ta a raga.

Zuwa yanzu Kudus ya zura kwallo 24 daga wasa 51 da ya buga, sannan ya taimaka an ci kwallo bakwai.

Kungiyoyi irin su Chelsea da Liverpool sun yi zawarcin dan wasan amma ya zabi tafiya West Ham don samun damar buga kwallo sosai.

A sannu dan wasan ya fara sace zuciyar magoya bayan West Ham, inda a lokuta da dama idan ya dauki kwallo ake fara rera wakoki da sunansa ana ta shewa.

6. Andre Onana

Bajintar Andre Onana dan kasar Kamaru a kakar da ta wuce ta shigar da shi jerin Zakarun Masu tsaron raga a Nahiyar turai.

Onana haziki ne kuma kwararre ba a iya tare kwallo ba, har ma da sarrafa ta da kafa da kuma taimaka wa ’yan wasan baya, inda suke samun nutsuwa daga barazanar abokan hamayya.

Hasali ma, Onana yana murza leda tamkar dan wasan baya ko na tsakiya — abun da aka matukar so a salon kwallon zamani.

Ya ba da babbar gagarumar gudumammawa wajen kai kungiyar Inter Milan wasan karshe na Gasar Zakarun turai a 2023.

Kokarinsa a 2023 ya sa Manchester United ta dauko shi daga Inter Milan kan kudi fam miliyan 40.

Sai dai kash! tun da ya koma Manchester United ta-barbare masa, inda ya zama kamar kawndo, da an buga kwallo sai ta shige raga.

7. Sadio Mane

Kyaftin din Senegal kuma dan wasan gaban Al Nasrr da ke Saudiyya, kodayaushe yana zama jagora wajen fitar da kasarsa kunya.

Mane shi ne dan wasan da ya taimaka wajen kai Senegal Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 a Qatar, amma rauni ya hani shi buga wasa a gasar.

Bayan ya raba gari da Liverpool ya koma Bayern Munich a Jamus, amma abubuwa ba su tafi yadda ake so ba.

Daga nan ya koma Al Nasrr a Saudiyya inda ya hade da Cristiano Ronaldo, ya sake warwarewa ya ci gaba da jan zarensa.

8. Taiwo Awoniyi

Taiwo Awoniyi, suna ne da ya fice a bakin masu sharhin kwallon kafar gasar Firimiyar Ingila, inda kowa ke yabon dan wasan dan asalin Najeriya da ke taka leda a kungiyar Nottingham Forest.

Dan wasan ya taimaka kungiyarsa wajen rashin fadawa gasar gajiyayyu kuma a bana, ya kuma bi sahun Salah inda ya zura kwallo a wasa bakwai a jere.

Mai shekaru 26, ya buga wasa 38 a bana sannan ya zura kwallo 15 a raga sannan ya taimaka wajen zura kwallo uku.

9. Kelechi Iheanacho

Kelechi Iheanacho dan wasan tsakiyar Super Eagles da kuma Leicester City da ke Ingila ne.

Duk da cewa kungiyarsa ba ta yi nasarar samun gurbin zama a gasar Firimiyar Ingila a bana ba, amma yana cikin wadanda ake yaba kwarewarsu a Ingila.

Dan wasan tsakiyar ya buga wasa 47 a 2023, sannan ya zura kwallo 12 a raga sannan ya taimaka an ci bakwai.

 

Sai dai a yanzu dan wasan ba kullum ake fara wasa da shi ba a kungiyar Leicester City.

A Najeriya kuwa dan wasan an mayar da shi tsakiyar fili inda yake taka wasa a matsayin lamba 10, wanda yake raga bayan ’yan wasan gaba kuma a wannan sabon gurbi da aka masa dan wasan yana nuna kwarewa.

10. Sofyan Amrabat

Dan asalin kasar Maroko ya nuna bajinta a Gasar Kofin Duniya ta 2022, sannan ya zama daya daga cikin zakarun kungiyar Fiorentina da ke Italiya.

Ambarat ya kasance jigo ne a tawagar ’yan wasan Maroko wanda hakan ya sa Manchester United ta dauke shi a matsayin aro daga kungiyar; ko da yake abubuwa ba su tafi yadda ake so ba a United.

Dan wasan tsakiyar ya taimaka wa Fiorentina musamman a gasar UEFA Conference League inda ya taimaka mata wajen raba kwallo da yake yi a tsakiyar fili.

Dan wasan tsakiyar ya buga wa kungiyarsa da kasarsa wasanni 60 a 2023 kuma taka rawar gani sosai.