Ƙasar China ta bai wa Afirka tallafin Yuan biliyan ɗaya da kayan aikin sojoji, don magance matsalolin tsaron da suka nahiyar.
Ministan Harkokin Wajen Sin, Wang Yi ne, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.
- An kashe mutum 3 bayan matsafa sun kai farmaki a Bayelsa
- Daga ƙasashen waje Boko Haram ke samun makamai da kuɗaɗe —Shugaban sojoji
Wang, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa wajen magance matsalolin tsaro.
Ya ce China tana da niyyar yin aiki tare da Afirka don bunƙasa zaman lafiya, tsaro, da ci gaba, tare da ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin China da Afirka.
“A matsayin wani ɓangare na wannan tsari, China za ta bayar da tallafin kayan soji na Yuan biliyan ɗaya ga ƙasashen Afirka,” in ji Wang.
“Haka kuma, za mu horas da sojoji 6,000 da jami’an ’yan sanda da na tsaro 1,000 daga ƙasashen Afirka.
“China za ta ci gaba da goyon bayan rundunar tsaron gaggawa ta Afirka da kayan yaƙi da ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya.”
Wang, ya tabbatar da cewa goyon bayan China ya shafi kare muradun Afirka a matakin duniya, musamman a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ya ƙara da cewa ƙasar za ta ci gaba da mara wa Afirka baya kan neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya tare da bayar da gudunmawa ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya a nahiyar.
“Najeriya tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Yammacin Afirka da yankin Sahel,” in ji Wang.
“China za ta mara wa Najeriya baya wajen haɗa kai da ƙasashen yankin don ƙarfafa hadin gwiwa da samar da zaman lafiya.”
Ambasada Tuggar ya bayyana ƙudirin Najeriya na yin aiki tare da China wajen ƙera kayan soji a cikin gida, don rage dogaro da saye daga ƙasashen waje.
Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa wajen magance matsalolin tsaro da tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.
“Najeriya koyaushe tana kasancewa jagora a Afirka, kuma muna girmama haɗin kai da ƙasashen kamar China don tabbatar da zaman lafiya da tsaro,” in ji Tuggar.
Wannan haɗin gwiwar ya nuna yadda China ke ƙara samun tasiri a Afirka tare da ƙudirin ƙarfafa ƙarfin nahiyar wajen magance matsalolin tsaro da kuma bunƙasa ci gaba.