✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dabbobi 90 daga hannun dan fashi a Kaduna

An kama wani da ake zargin barawon shanu ne aka kwato dabbobi 90 a hannunsa a Kaduna

An kama wani da ake zargin barawon shanu ne aka kwato dabbobi 90 a hannunsa a Jihar Kaduna ranar Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya da misalin karfe 11.30 na dare ’yan sanda da ke sintiri a kusa da Kasuwan Dole a yankin Millennium City suka yi nasarar cafke wanda ake zargin.

Hassan ya bayyana cewa ana zargin mutumin da hannu a satar shanu 65 awaki 25 kuma a yayin bincike bayar da gamsasshen bayani kan dabbobin.

Ya kara da cewa yankin ya samu kwanciyar hankali yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri don tabbatar da tsaron al’umma.