Mayakan kungiyar ISWAP sun kwashi kashinsu a hannun sojoji a lokacin da ’yan kunigyar suka kai wani hari a yankin Gajiram da ke Jihar Borno.
’Yan ta’addan sun fashe ne daga yankin Gubio/Magumeri inda suka far wa sansanin sojoji da ke kan hanyar Maiduguri da Monguno mai nisan kilomita 135.
- Najeriya za ta tura sojoji 205 samar da tsaro a Gambia
- PDP: ‘Masu neman takarar Shugaban Kasa 2 sun yi asarar kudin fom dinsu’
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, a ranar Juma’a a Maiduguri, Shugaban Civilian JTF, Modu Aisami ya bayyana cewa, “’Yan ta’adda sun kai hari Gajiram da sanyin safiyar Juma’a.”
Ya kara da cewa, maharan sun taso ne a cikin ayarin motoci dauke da manyan bindigogi da babura domin auka wa sojoji da fararen hula da ke kan hanyar.
Modu Aisami ya kara da cewa an kuma kashe wasu ’yan ta’adda da ba a tabbatar da adadinsu ba a cikin sama sa’o’i guda da aka shafe ana fatattakar su a garin Gajiram.
Modu ya kara da cewa sojoji sun dakile wannan hari na su ne ta amfani da dakarun kasa da kuma ta sama, har ta kai ga kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi a jikinsu.
Ya ce jirgin yakin na Super Tucano ya yi ruwan bama-bamai kan motocin ’yan ta’addar, inda ya kashe da dama daga cikinsu, yayin da wasu suka samu raunuka.
“An ga motoci da aka girke wa bindigogi guda biyu dauke da ’yan ta’adda 12,” in ji shi.
Ya kara da cewa wasu daga cikinsu sun samu raunuka ne da gawarwakin da aka jibge a cikin yankin Gambo Yakku a Karamar Hukumar Gubio.