’Yan bindiga da ake kyautata zaton mambobin haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB ne sun kashe Baturen ’Yan Sanda, CSP Fatmann Dooiyor.
Dooiyor dai shine Baturen ’Yan Sanda (DPO) na yankin Omuma, mahaifar Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da ke Karamar Hukumar Oru ta Gabas a Jihar.
- COVID-19: An samu sabon samfurin Delta guda 10 a Najeriya – NCDC
- Garkuwa da dalibai: An sake rufe makarantu a Kaduna
Rahotanni sun ce ya rasa ransa ne a lokacin da yake kokarin mayar da martani ga maharan.
Lamarin dai na zuwa kwana daya bayan da yunkurin gurfanar da jagoran kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kani a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
A cewar wata sanarwar da Kakakin ’Yan Sandan Jihar ta Imo, CSP Mike Abattam ya fitar, an sami nasarar kashe shida daga cikin maharan, yayin da 11 kuma suka shiga hannu.
Kakakin ya ce gungun maharan a kan motoci uku sun kai hari yankin amma sun fuskanci tirjiya daga ’yan sanda, karkashin jagorancin ACP Benjamin Abang.
Abattam ya ce, “Muna samun labarin tahowarsu, tawagarmu bata yi wata-wata ba ta yi musu kwanton bauna inda ta hallaka shida daga cikinsu, ta kuma kama 11.
“Sai dai a sakamakon harin, DPO na yankin CSP Fatmann Dooiyor ya rasa ransa.
“Daga bisani kuma jami’anmu sun sami nasarar kwace motoci ukun da suka kawo harin da su, ciki har da wasu kirar Toyota SUV masu lambobin Abia MBL517AT da kuma LAGOS , JJJ984EL da kuma wata Jif kirar Lexus mai ruwan madara wacce babu lamba a jikinta,” inji sanarwar.
Ko a farkon wannan shekarar dai sai da ’yan IPOB din suka kai hari yankin inda suka kashe mai gadin gidan Gwamnan a garin sannan suka cimma masa wuta.