Wasu da ake kyautata zaton matakan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne sun hallaka wasu sojojin Najeriya da ke aiki a yankin Kudu maso Gabas.
Mahara sama da 15 ne dauke muggan makamai suka kai hari kan sojojin da ke sintiri a mahadar Obikabia da ke Aba a Jihar Abia a ranar Alhamis.
Rahotanni daga yankin sun ce bayan ’yan IPOP din sun harbe sojojin ne suka sa wa motar sintirin wuta.
Mai magana da yawun haramtacciyar kungiyar, Emma Powerful, ya ayyana 30 ga Mayu a matsayin ranar juyayin tunawa da mayakan Biafra.
Ya kuma umarci ’yan yankin Kudu maso Gabas su zauna a gida dole, domin jinjina ga mayakan Biafra da sojojin Najeriya suka hallaka a yakin basasa.
- Dalibai 30,000 sun yi nasarar rancen kudin karatu a kwana 6
- Ainihin abin da Gwamnan Kano suka tattauna da Nuhu Ribadu
A wannan rana, ’yan ta’addar sun tilasta an rufe gidajen mai, da bankuna, da manyan gidajen cin abinci, da manyan kantuna a fadin kudu maso kudancin Najeriya.
Jama’ar jihohi biyar da ke yankin sun yi biyayyar dole ne saboda fargabar ta’addancin ’yan kungiyar ta IPOB.
Da yake mayar da martani game da harin, Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Benjamin Kalu, ya ce “Wadanda suka aikata wannan danyen aiki ba su da wani dalili.
“Rashin gaskiya ce kawai tsagwaronta, da zalunci, da rashin imani da kuma rashin la’akari da halin rayuwa.”
Kalu ya jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ya kuma bai wa da hukumomin sojan Najeriya tabbacin daukar matakan da suka dace don taimakawa wajen bankado wadanda suka kitsa harin domin hana sake samun irin haka a nan gaba.