’Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun ƙona gidaje 23 a yankin Egwuma da ke Ƙaramar Hukumar Agatu ta Jihar Binuwai.
Mazauna yankin sun bayyana cewa mutane da dama sun tsallake rijiya da baya a harin da raunukan harbi.
Shuagaba Ƙaramar Hukumar Gari, Philip Ebenyakwu, ya shaida wa ’yan jarida a Makurɗi, babban birnin jihar, cewa mutane uku ne suka tsira da raunukan harbi.
Ya Bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, kuma waɗanda aka ji wa raunukan suna samun kulawa a asibiti.
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Fara Kananan Sana’o’i A Najeriya
- Gwamnatin Kano ta janye dokar hana fita gaba ɗaya
Ya ce, “Makiyaya ɗauke da makamai daga Jihar Kogi suna yawan kai hare-hare a Agatu ta Yamma.
“Yankin da aka kai wa hari yana iyaka da Jiahr Kogi, kuma yana yawa fuskantar barazana.
“Ranar Lahadi makiyayan suka kai hari a yankin Egwuma, inda suka ƙona gidaje 23 suka sace babura biyu.”
Duk da haka, Ebenyakwu, ya yaba wa jami’an tsaron da aka tura yankin.
Ya bayyana cewa a ranar Asabar wani sojan ruwa ya ƙwace jirgin ruwa da ’yan bindiga ke shigowa a kai daga Jihar Nasarawa.
Wakiliyarmu ta yi ƙokarin tattaunawa da kakakin ’yan sanda a Jihar Binuwai, SP Catherine Anene, amma ba ta amsa kiran waya ko rubutaccen saƙon da aka tura mata ba.