✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashin daji sun sace matafiya 20 a hanyar Kontagora

Aƙalla matafiya 20 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Mariga zuwa Kontagora a Jihar Neja.

Aƙalla matafiya 20 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Mariga zuwa Kontagora a Jihar Neja.

Shugaban majalisar dokokin jihar, Barista Abdulmalik Sarkin-Daji, ya ce ’yan ta’addan sun yi awon gaba da mutanen ne daga was motoci biyar a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun yi aika-aikan bayan sun tare hanyar da ta taso daga Baban-Lamba zuwa Beri.

Ya sanar da hakan ne a martaninsa ga rundunar sojin Nijeriya da ta musanta samuwar ayyukan ’yan ta’adda a sansanin horo soji da ke yankin ƙananan hukumomin Kontagora da Mariga.

Shugaban majalisar ya ce iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su sun sha kai wa ’yan bindiga kuɗin fansa a yankin.

An zargin ’yan bindiga suna amfani da dajin filin barikin sojoji na Kontagora a matsayin mafaka, inda suka addabi mazauna ƙauyukan da ke maƙwabta da su.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa matafiyan da aka sace ranar Alhamis ma an shige da su ne dajin barikin, wanda ke matsayin sansanin horo ga sojojin rundunar makaman atilare.

Don haka ya bukaci sojoji su bincika su samu sahihan bayanai domin fatattakar ɓata-garin.

Ya bayyana cewa a matsayin ’yan majalisa na wakilan al’umma, su ake kawo wa korafi al’ummominsu, kuma ba sa fitowa su yi magana sai sun tabbatar sahihancinsa.

Saboda haka ya ce maimakon sojoji su tsaya yin ƙorafi da ƙaryata maganar, kamata ya yi sun zurfafa bincike su ɗauki matakin da ya dace.