✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe sojoji sun sace ɗan ƙasar waje a Zamfara

Harin shi ne irinsa na biyu a kusan lokaci guda a hanyar da ake wa laƙabi da Isra'ila saboda yawan ta'addacin ’yan fashin daji

’Yan bindiga sun kashe sojoji uku da wasu mutane hudu, suka sace wani ɗan ƙasar waje a babbar hanyar Funtua zuwa Gusau.

Sojojin suna rakiyar injiniyoyin ƙasashen waje da ke aikin gine-gine a kan titin ne lokacin da’yan bindigar suka far musu a yankin ’Yandoton-Tsafe da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna brahim Umar, ya bayyana cewa ya ce, ’yan bindigar da suke kan babura sun bude wuta ne a kan ma’aikatan a safiyar Alhamis.

A cewarsa, duk da ƙoƙarin sojojin na dakile harin, an kashe mutane kusan bakwai ciki har da sojoji, kuma an yi garkuwa da wani injiniya ɗan ƙasar waje.

Harin shi ne irinsa na biyu da ’yan bindiga suka kai a kusan lokaci guda a wannan hanya a safiyar.

Sace matafiya

An kai na farko ne a ƙauyen Kucheri da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda gungun wasu ’yan bindiga suka tare hanyar Funtua zuwa Gusau, suka kashe mutane da dama suka sace matafiya da ba a bayyana adadinsu ba.

Shaidu sun ce ana kyautata zaton duka hare-haren, Ɗan Yusuf, wani shahararren jagoran ’yan bindiga, kuma ƙanin ɗan fashin nan mai suna Ado Alliero, ne ya shirya su.

Wani mazaunin garin Kucheri ya ce ’yan bindigar sun zo ne a kan babura, suka ɓoye kansu a cikin dazuzzukan.

Daga nan ne suka yi wa motoci kwanton ɓauna a wani yanki da hanyar ta lalace a kusa da ƙauyen Kucheri.

“Direbobi suna tafiya a hankali a wannan wurin da ya lalace, wanda ’yan fashin suke amfani da shi wajen kai wa motocin hari su sace fasinjoji,” in ji majiyar.

A baya-bayan nan titin Funtua zuwa Gusau ya zama tarkon mutuwa ga matafiya da sauran masu amfani da shi.

Direbobi sun koma kira tsakanin Funtua da Tsafe mai tsawon kilomita 50 da sunan “Isra’ila” a  saboda ta’addancin da ke faruwa, na sace-sacen mutane da kuma kai hare-hare a kan al’ummomin.

Yankin ya kunshi ƙauyuka da garuruwa a jihohin Katsina da Zamfara.

Duk da ƙarin shingayen binciken sojoji da aka kafa a tsakanin Kamfanin-Mailafiya da Tsafe, kusan kullum sai ’yan bindigar sun kai hari a  yankin.